Dattawan Arewa Sun Mai Da Martani Yayin Da Jihar Ondo Ta Gabatar Da Fara Rera Taken Kasar Oodua A Makarantu

 Majalisar zartarwa ta jihar a kwanan nan ta amince da  taken Oduduwa wanda ke gabatar da kyawawan halaye,  da al'adun yarbawa. 

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a ranar Lahadi ta bayyana gabatar da fara rera waƙar taken  Oduduwa a makarantun sakandare na gwamnati a cikin jihar Ondo a matsayin mummunan rauni ga zamantakewar Nijeriya a matsayin dukulalliyar kasa.

 

Gwamnatin jihar, a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan wata 6, 2021, wanda Tolu Adeyemi, sakatare na dindindin na Hukumar Kula da Koyar da Ilimin na Jihar Ondo ya sanya wa hannu wacce aka aikewa  dukkan daraktocin shiyya na TESCOM da shugabannin makarantun sakandaren gwamnati a jihar, ya zama tilas a karanta waƙar Taken  Oduduwa a duk  makarantun sakandaren gwamnati a duk faɗin jihar.

 

Majalisar zartarwa ta jihar a kwanan nan ta amince da  taken Oduduwa wanda ke gabatar da kyawawan halaye,  da al’adun yarbawa.

 

Akeredolu ya ce za a rika rera wakar  taken bayan an rera taken kasa a  dukan makarantun jihar.

 

Da yake tsokaci kan lamarin a ranar Lahadi, Daraktan Yada Labarai da Ba da Shawara na Kungiyar Dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce: “Idan wannan gaskiya ne, to yana nuna mummunan rauni ga kasancewarta a matsayin dunkulalliyar kasa da mutanen da suka rantse  zasu taimaka mata  kuma ka kare ta suka ka yi ”

 

Ya ce ba za a iya kare irin wannan matakin ta kowace fuska ba face tsokana da wasa a dandalin da ke neman fadada barnar da rashin kadin kai tsakanin ‘yan Najeriya ta hanyar kabila da yanki ke yi.

 

Ya ce: “Akwai take guda daya da ya kamata ’ ya’yanmu su rera kuma su gane. Idan akwai wasu alamomin da ke nuna  muhimmancin al’adu da ya  kamata a san muhimmancinsu ,kada a  daga matsayinsu  zuwa matsayin taken ƙasa, ko ma a fifita su ba.

 

“Idan  gwamnatin tarayya tana kan kafafunta na kare iyakokin hadin kanmu da mutuncin kasa, ya kamata ta kalubalanci wannan a kotu. Ta kuma daukaka matakanta na sanya ido kan yadda ‘yan siyasar da  ke cin gajiyar kundin tsarin mulkinmu wadanda ke goyon bayan abubawa masu hatsari da ka iya haifar da rashin hadin kai.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More