Daukaka karar Atiku Shin kuna ganin zai samu nasara?

Dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben da ya gudana na ranar 23 ga Fabrairu 2019 wato  Atiku Abubakar ya daukaka kara a kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe kan hukuncin da ta zartar na tabbatar da nasarar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP da kuma Atiku Abubakar  sun jajirce cewa kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskure wajen amincewa da cancantar Buhari a matsayin zabbaben shugaban Najeriya, kamar yadda daya daga cikin lauyoyin PDP Mike Ozekhome (SAN) ya sanarwa manema labarai.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More