Daya daga cikin masu tsaron lafiyar Shugaba Buhari na Najeriya ya rasu

Mai taimakawa Shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya fitar sa  sanarwar cewa,  Lawal Mato ya rasu ne sakamakon ciwon suga da ya shafe  fama da ita shekaru uku, a shafinsa na Twitter.

Sanarwar ta bayyana cewa Mato ya  rasu ne ranar Talata.

Mato ya dade yana aiki da Shugaba Buhari tun kafin ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2015, kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

BBC ta rawaito  cewa, wata ‘yar uwar mamacin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce mana ya rasu ne a Kano bayan ya dan yi fama da rashin lafiyarsa ta ciwon suga a wani asibiti da ke birnin.

Dan ainihin garin Maigatari na jahar Jigawa, kuma a can aka yi jana’izarsa da yammacin Talata.

Ya mutu ya bar mata daya da yara bakwai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More