Dokar hana amfani da Keke Napep a Lagos ta  fara aiki

A ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu  ne mazauna birnin Lagos da ke  kasar Najeriya suka wayi gari da haramcin da gwamnatin jahar ta yi musu na hawa babur mai kafa uku, wanda aka fi sani da Keke Napep, Marwa, ko  A Daidaita Sahu.

Wakilalin BBC  ya samu damar daukar  hotu kai tsaye, wanda ke nuna mutane a tsaye cirko-cirko suna jiran ababen hawa.

Mafi akasari da al’ummar jahar sun fi yin amfani da wadannan babura wajen yin sufuri a cikin garin birnin, da kuma yankuna kauyukan.

A watan gabata ne gwamnati ta haramta amfani da acaba Opay da GOKADA da Maxkeke.

Gwamnatin jahar ta bayyana cewa ta haramta aikin masu baburan ne saboda karya doka da hadurran da masu sana’ar ke haddasawa.

Sai dai  hakkan ya sa masu haya da baburan sun yi zanga-zanga domin nuna bijirewarsu na haramta aikin nasu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More