Dokar hana fita a jahar Kano zata fara aiki daga yau

Daga cikin matakan da  Gwamnatin jahar Kano ta  dauka dun gudun yaduwar Coronavirus a jahar, harda na hana fita na tsawun mako guda, wanda dokar zata fara daga misalin karfe 10:30 na daren Alhamis 16 ga watan Aprilu 2020.

Gwamnan  Abdullahi  Umar Ganduje ya ya haramta wa ‘masu tukin A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya’, inda daga bisani shugaban kungiyar a daidaita sahu ta jahar Kano ta roki alfarma daukar mutane 2.

Yayin da gwamnan ya amince da hakan.
Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.

Kazalika, gwamnatin jahar ta ce za ta dauki matakai na rufe wasu kasuwanni inda  za a bar kasuwannin da ke sayar da kayan abinci da sauran kayan bukatar gaggawa su ci gaba da budewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More