Dokar hana fita na iya dawowa a Legos – gwamna Sanwo-Olu

Gwamnatin  jahar Legas ta yi gargaɗin cewa za ta kuma kafa  dokar hana fita, idan har mutane suka ci gaba da saba sharuddan da aka saka bayan sassauci a kan dokar  ta fita hana fitar.

Gwamnan jahar Babajide Sanwo-Olu ya ce duk da aikin faɗakar da al’umma da aka yi amma abin takaici sai ka ga dandazon jama’a a bankuna da kasuwanni na sassan jahar suna saɓa ƙa’ida.

Za a tilasta mana ɗaukar mataki marar daɗi na kulle  a jahar gaba ɗaya idan har mutanen Legas suka ci gaba da saɓa dokokin.Inji gwamnan.
Ya kuma ce za a kama duk ɗan okada da kuma motocin fasinja da ke zirga-zirga idan suka ci gaba da saɗa dokokin da aka saka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More