Dokar zaman gida zata fara aiki  a jahar Borno

Gwamnan jahar Borno, ya   fitar da  sanarwa a jiya  wacce ke cewa, gwamnatin su zata sanya dokar zaman gida daga ranar Laraba dan gudun yaduwar cutar Covid19, yayin da cutar ta bulla a karshen makon da ya gabata.

Mai magana da yawun gwamnan jahar, Isa Gusau, ya ce an bai wa ‘yan jahar kwana biyu ne domin  su shirya kafin ranar Laraba lokacin da za a rufe jahar.

Kafin bullar cutar a jahar dai gwamnatin jahar ta sha kokarin daukar matakan kariya na dubban ga  ‘yan gudun hijrar da ke zaune a sansanoni daban-daban a fadan jahar ta Borno.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More