Duk wadda aka samu rika da bindiga Ak-47 ba bisa doka ba a harbeshi

duk wadda aka samu rika da bindiga Ak-47 ba bisa doka ba a harbeshi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis a Abuja ya kara Jaddada cewa ya bada Umarni ga Shugaban nin Jami’an tsaro kan suyi ba dai dai ba ga duk wani ɓata gari, ciki harda Umarnin a harbe duk wani da aka samu rike da bindigar Ak-47 ba bisa doka ba.

Shugaban kasa yayi wannan Magana ce a gurin taro da Majalisar Sarakunan Gargajiya na ƙasa a fadar Gwamnati, wanda Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku da Sarkin Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi suka Jagoranta.

Taron ya samu halartan Manyan Shugaban nin Tsaro wanda suka hada da Mai bada Shugaban kasa Shawari kan harkokin Tsaron kasa Majo Jeneral Babagana Monguno Mai ritaya, da Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa Mohammed Adamu, da Babban Daraktan Hukumar Tsaro na farin kaya Yusuf Bichi da Babban Darakta na Hukumar Tara bayanan Sirri na ƙasa Ambasado Ahmed Rufai Abubakar.

Shugaban kasa, wanda ya sanar da dakin taro kan kokarin da Gwamnati take yi don inganta harkokin tsaro a Ƙasa, yace Gwamnatin sa ta samu nasarori a yankin Arewa maso gabas da Kudu maso Kudu ya Ƙasar.

“to amma abun Mamaki shi ne abunda yanzu ke faruwa a yankin Arewa maso yamma inda Mutane iri guda masu Al’adu iri daya suke kashe Junan su, sace Dabbobin kiwon su da kuma ƙona kaddarorin su.

” A sakamakon haka, Mun yi taron na Majalisar Tsaro na kasa na tsawon Sa’oi Hudu wanda Ministan Harkokin Cikin Gida daba Tsaro dana Harkokin Kasashen waje da Manyan Hafsoshin Tsaro, da Babban Hafsan tsaro na kasa da Babban Sufeton Ƴan sanda na ƙasa da Sauran su kuma mun fada Umarni da yawa da suka dace,

” Amma abu guda kawai dayashiga kunnen Manema Labaru wanda Ni da kaina na karanta shi ne cewa wanda aka kama da Bindiga Ak-47 a harbe shi.

‘Wanda kuma saboda bisa doka dama ya kamata bindiga Ak-47 ta zamo tanada Rijista kuma Jami’an tsaro ne kawai ake basu.

‘Mun kulle iyakoki tsawon wasu Shekaru to amma rahotannin Sirri da ni nake samu a kullum shine cewa wa dan da ke aikata Sace Mutane da kashe kashe da Sauran miyagun aiyuka har yanzu suna da makamai da Albarusai,” Cewar Shugaban.

Shugaban kasa ya nuna rashin jin dadi kan hare hare kan Ofishoshin ‘Yan sanda da kisan Jami’an Tsaro da masu taka doka keyi, yayi Gargadi cewa babu fa wani mai muradin zuba jari da zai sanya Jarinsa a inda babu zama lafiya.
Shugaba Buhari ya kuma kara nuna bukata ga Sarakunan gargajiya suyi amfani da damar su da matsayin su don hada garurukan da suke Jagoranta don mara baya ga kokari da Gwamnati keyi don tabbatar da Tsaro da Zama lafiya.
Shugaban yayi roko ga Sarakunan Gargajiya da suyi imfani da damar da suke da shi ta hanyar mai kyau don tallafawa Gwamnati don zakulo wa dan nan, da basu da buri yada wuce jawo fitina da lalata abunda Al’umma ke rayuwa da Iyali a Fadin kasa.

Shugaban, wanda ya saurari bayanai daga Wakilai Sarakunan Gargajiya daga dukkanin shiyoyin Siyasar kasa guda shida, yayi Alkawari cewa Gwamnatin sa zataci gaba da mara baya ga aiyuka tare dasu don tabbatar da Daidaituwar Zama lafiya.

Ya kara Jaddada Umarnin daya bada wa Sabbin Hafsoshin Tsaro da aka bada na kokarin ganin sun daidaita harkokin tsaro, Shugaban kasa ya lura cewa za’a iya samun nasara ce kawai hadin kai da aiki tare da sarakunan Gargajiya da Hukumomi, wanda suke rike da muhimman matsayi cikin Al’umma.

“Da irin rawa da zaku taka da Matsayin ku wanda Cikin Tarihi Shekaru Daruruwa ya nuna, Al’umma suna nuna muku kamsu da yadda kuma kuna samar musu da jin dadi da basu Shawari dai dai da yadda tsarin Al’adar mu yake.
” Kun samu wata ma hada na dukkan yankunan mu. Babu wanda ya dace yayi imfani da karfi ikon Shugabancin ku gurin tabbatar da cewa Mutanen da suka zo garuruwan ku ko don Kasuwanci, Jin dadi ko wata Dalila ta gaskiya an basu kariya da zasu ji kamar a gida suke,” Inji Shugaban.

Cikin Jawabin daban daban, Sarakunan sun kara karfafa bukatar ga Masarautun aka sanya su taka rawar su, Musamman akan harkar tsaro da zama lafiya, dai dai da yadda dokar kasa ta tsara dama kuma Sanya sharadodin dokokin Majalisar kasa da Sauran dokoki.

Wadan dan Sarakuna sunyi tsokaci a gurin taron wanda suka hada da, Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Oani na Ife, da Sarkin Onitsha Obi, da Sarkin Nnaemeka Achebe, da Sarkin Nufe Alhaji Dakta Yahaya Abubakar, da Sarki Jaja na Opbo Dakta Dandeson Douglas Jaja, da Sarkin Bauchi, Dakta Rilwan Sulaiman Adamu, da Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Iliyasu da kuma Sarki Alawe-Ekiti Adebanji Ajibade Alabi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More