Duk Wanda Ya Bani Cin Hanci Ya Fito In Ya Isa – Magu

Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu ya fadawa kwamitin binciken da ke bincikensa cewa bai taba karbar rashawa daga kowa ba a rayuwarsa.

A zaman da aka yi a ranar laraba, Magu ya kalubalanci duk wanda ya taba ba shi cin hanci wanda ya karba ya ce “ya fito fili ya fuskance ni a gaban kwamitin Justice Ayo Salami”.

Magu ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa zargin da ake yi na cewa ya ba wata da ake zargi Hima Aboubakar, ‘yar asalin kasar Nijar damar tserewa daga tuhumar ta.

A ranar Litinin din nan ne, tsohon Shugaban Hukumar ta EFCC da aka dakatar ya bude kariya ga zarge-zargen da ake Masa.

Kwamitin binciken ya ba shi damar samun lauyoyi biyu ne kawai da za su tsaya masa a lokaci guda. Wahab Shittu da Aliyu Lemu sune suke wakiltar shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More