
EFCC ta afka wa gidan Shehu Sani dan gudanar da binciki
Rahotunin sun nuna cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki wato (EFCC) sun ziyarci gidan tsohin sanatan jahar Kaduna ta tsakiya wato kwamred Shehu Sani domim gudanar da bincike.
Jami’an hukumar EFCC sun dira gidan tsohon Sanatan dake unguwar Maitama da misalin karfe 2:00, kafin suka wuce gidansa na Wuse II da misalin karfe 3:00 duk a babban birnin tarrayar Abuja da yammacin yau Laraba 8 ga watan Janairu 2020.
A makon da ya gabata ne dai hukumar EFCC ta cafke Shehu Sani bisa zarginsa da zambar wani dan kasuwa a Kaduna, bisa kudin naira miliyoyan 7.2.
Tuni tsohon Sanatan ya bayyana cewa wasu makiyansa na siyasa ne suka tunzura dan kasuwar har ya shigar da korafinsa a ofishin EFCC domin ganin cewa an tozarta shi a bainin jama’a.