EFCC ta bawa VON ginin biliyan 4.5 data kwata a gurin Alex Badeh

 

Hukumar Yaki da Rashawa EFCC ta mika wa Muryar Najeriya (VON) wani katafaren gini mallakar tsohon babban hafson tsaro na Najeriya wato  Air Marshal Alex Badeh, a jiya Laraba 17 ga watan Yuli 2019.

Kudin ginan ya kai kimanin naira biliyan 4.5 da ke Plot 1386 Oda Crescent, Off Aminu Kano Crescent, Wuse 2 dake babban birnin tarayyar Abuja.

Mukadashin Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya ce idan aka samu nasarar yaki da rashawa a kalla kashi 70 cikin 100, za a warware mafi yawancin matsalolin da ke adabar kasar ta Najeriya.

Shugaban sashin hulda da jama’a Mista Tony Orilade ya fitar da sanarwar cewa ,ta Katafaren ginin yana daya daga cikin kadarorin da aka kwato daga hannun  marigayi tsohon babban hafson tsaro na kasar, Alex Badeh kuma aka mika ga gwamnatin tarayya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More