Dalilin da yasa EFCC ta cafke dan tsohon gwamna Abubakar Audu a Legas

Jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC sun cafke Muhammed Audu, dan gidan marigayi tsohon gwamnan jahar Kogi Abubakar Audu, a ranar Talata 18 ga watan Febrairu 2020.

Hukumar EFCC ta cafke shine bisa zargin laifin zamba cikin aminci, karkatar da miliyoyin daloli da biliyoyin Naira da aka baiwa hukumar kwallon kafar Najeriya kyauta dan amfanin kansa.

Bincike ya bayyana cewa ya yi amfani da kamfanoninsa biyu Mediterranean Hotels Limited da Mediterranean Sports wajen karkatar da kudaden, kuma ya kasa yin bayani a kansu.

Za’a gurfanar da Muhammad Audu a kotu muddin aka kammala bincike.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More