EFCC ta kama tsohon shugaban majalisar dokoki ta Kano

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC  ta kama tsohon shugaban majalisar dokokin jahar Kano kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar yanzu wato  Isiyaku Ali Danja.

Wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban sashen yada labaranta, Tony Orilade, ta ce an kama shi ne bisa zarginsa da yin amfani da ofishinsa ba yadda ya kamata ba da kuma sace wasu kudade da aka ware domin ayyukan mazabu.

Hukumar ta dauki matakin ne sakamakon wata takardar korafi da aka shigar cewa an karkatar da wasu kudaden haraji da suka kai sama da N1.5b daga asusun gwamnatin jahar Kano.

Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi.

Sai dai a sanarwar EFCC ba ta bayyana sunan wanda ya shigar da karar ba.

EFCC ta ce za ta shigar da kara gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

A makon da ya gabata ne  EFCC ta kama kwamishinan ayyuka na musamman na jahar Kano,  wato Mukhtar Ishaq, bisa zargin karkatar da wasu kudaden karamar hukumar birni lokacin da yake shugaban karamar hukumar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More