EFFC ta dira gidan tsohon gwamnan Legos bincike

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC a yau Talata 20 ga watan Agusta 2019, sun shiga gidan tsohon Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, inda suka binciki gidan duk a cikin binciken rashawa da ake gudanarwa akansa. Jaridar Premium Times ta rahoto daga kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade cewa ana bincikar Mista Ambode akan zargin rashawa tun wasu yan watannin da suka gabata bayan barinsa Ofis.

An binciki gidan Mista Ambode dake kauyen Ekpe da misalin karfe 9:35 na safe a lokacin da Mista Orilade ya tabbatar da lamarin tare da bincikar gidan shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan wanda ke makwabtaka da Ekpe.

Ana zargin cewa an karkatar da Biliyoyin nairori cikin shekaru hudu da Mista Ambode yayi a ofis, kuma kwararru suna ta gudanar da ayyuka don warware duk lamarin da ya shafi zargin rashawar.

A makonni biyu da suka gabata aka gano wasu asusun bankuna dauke da biliyoyin kudi wanda ke da nasaba da Mista Ambode wadanda aka daskarar a yayin bincike
Mista Ambode ya musanta cewar yana da nasaba da asusun da kuma duk wasu zarge-zargen rashawa a lokacin da yake kan mulki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More