Eid el Kabir: Abubuwa 9 da suka kamata Musulmi ya yi a watan Dhu al-Hijjah

Malamai na ci gaba da fadakar da al’ummar Musulmi dangane da falalar kwanaki goman farko na watan Dhul Hijjah, bayan ayyana ranar Laraba a matsayin ranar farko ga watan wanda shi ne na 12 a tsarin kalandar Musulunci.

Musulmi dai na daukar kwanaki goman farko na wannan watan a matsayin mafi daraja a wajen Allah.

Hadisi ya zo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanaki goman farkon watan Dhu al-Hijjah.

Akwai kuma ibadu da dabi’u da Musulmi ke siffantuwa da su a cikin wadannan ranakun da suka haɗa da yin azumi da hawan Arfa da kuma layya domin neman kusanci ga Allah Ubangiji.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi wa BBC Hausa bayani kan muhimmancin watan na Dhu al-Hijjah da kuma abubuwan da ya kamata Musulmi su yi:

Kada a aske gashi da yanke farce

Abu na farko shi ne idan mumutum yana da niyyar zai yi layya, to daga daya ga watan Dhu al-Hijjah kada ya yanke farce kuma kada ya aske gashin jikinsa. Domin Allah (SWA) zai ba shi lada adadin yawan gashin kansa da kuma adadin tsawon faratansa har ya zuwa lokacin da zai yi layyarsa. Daga nan kuma sai ya je ya yi aski da yanke faratan nasa.

Azumin ranar Arfa

A cewar Sheikh Daurawa, abu na biyu shi ne, ana so mutum ya yi azumin ranar Arfa. Hadisi ya zo cewa azumin ranar Arfa yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da kuma wacce za ta zo.

Layya

Abu na uku shi ne ana so mutum ya yi layya. Yin layya koyi ne da Sunnar Annabi Ibrahim (ASW), wanda Allah ya umarce shi ya yanka dansa domin ya jarraba shi, ya ci jarrabawar har aka fanshi dan nasa da rago.

Manzon Allah ya sayi raguna guda biyu ya yanke, sannan ya ce duk wanda yake da hali ya yi layya.

Wannan layi ne
Sallar Idi

Ana so kuma mutum ya yi sallar Idi ranar ta Idi, kuma ya yi kwalliya da sabbin tufafi. Idan ba shi da sabbi ya sanya mafiya kyawu da yake da su. Ana bukata kuma ya kyautata wa iyalinsa, su ma ya saya musu sabbin tufafi idan da hali. Kazalika su fita a je sallar idi tare da mata.

Azumin watan Dhu al-Hijjah

Baya ga azumin ranar Arfa, ana so mutum ya yi azumi a wasu daga cikin ranakun watan na Dhu al-Hijjah tun daga farkonsa. Zai iya yin hakan ko da kuwa ana bi sa azumin watan Ramalana.

Yawaita sadaka

Akwai matukar muhimmanci mutum ya yawaita sadaka a watan Dhu al-Hijjah; misali, idan yana sadakar N1000, to ya kamata ya kara zuwa sama da haka, ko ma ya nunka idan yana da hali.

Wani karin abu shi ne, mutanen da ba za su je aikin Hajjin bana ba, za su iya amfani da wani kaso na kudinsu wajen sayen kayan abinci da tufafi su bai wa marasa karbi. Shi ma aikin sadaka ne.

Sada zumunta

Ana so Musulmi ya dage wajen yin zumunci da kai ziyara ga ‘yan uwa da abokan arzuki a wannan wata.

Yawaitar kabbara

Haka kuma ana so mutum ya yawaitar kabbar a wannan wata mai albarka. Yana da kyau a yi kabbarori nau’i daban-daban irin su Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha illalLah Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamdu

Hajj

Sannan ana so a wadannan kwanaki mutum ya je ya yi aikin Hajji ko Umrah.

Malamai sun ce wadannan ayyuka na ibada sun hade kusan dukkan rukunan Musulunci, shi ya sa ake kwadaitawa Musulmi su juri yinsu a wannan wata mai alfarma.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More