Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a kudu

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a wasu sassan kudanci kasa yayin da gamayyar kungiyar masu sayar da kayan abinci da masu sayar da dabbobi ke cigaba da yajin aikin kai kayansu zuwa kudancin kasa
Biyo bayan umarnin hana shigar da kayan abinci zuwa Kudancin kasa da Gamayyar Kungiyar Masu Sayar da Abinci da Masu Sayar da Adabbobi ta Najeriya, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin yau da kullun a wasu sassan jihar Enugu da jihar Abia.

 

Wani dillalin shanu a Orba, Karamar Hukumar Udenu ta jihar Enugu, Jonas Ndidiamaka, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa ci gaban ya shafi kasuwancin shanu a yankinsa.

 

Ya ce “Wannan ci gaban yana shafar kasuwancinmu saboda ba mu san abin da za mu yi ba idan dabbobin da muke da su suka kare.Farashin shanu a yanzu ya fi na lokacin Kirsimeti da ya gabata. Saniyar da ta kai N120,000 a lokacin Kirsimeti yanzu ana sayar da ita kan N160,000, yayin da wadanda aka sayar a kan N200,000 a da, yanzu ana sayar da su kan N280,000. ”

 

Hakanan, wani ma’aikacin banki a garin da ke kan iyaka zuwa Arewacin Najeriya, Obollo Afor, Ifeanyi Anigbo, yabkoka kan raguwar hada-hada.
Anigbo ya ce, akasarin abokan kasuwancin sa dillalan abinci ne kuma ci gaban ya shafi yawan mu’amalar da ya saba yi dasu.
A Aba, Jihar Abia, buhun albasar da a da ake sayarwa a kan N20,000 a yanzu ana sayar da shi kan N30,000.
Dillalan albasa a kasuwar Orie Ugba da ke Umuahia, wacce ta bayyana sunan ta da Matam Bala ta shaida wa jaridar Vanguard cewa, buhun albasar da ta sayo daga kasuwar Aba a makon da ya gabata an biya ta zuwa ranar Talata, kan kudi N30,000. Biyo bayan karin kashi 50 na farashin a wurin siyan, adadin da a da ake siyarwa akan N200 yanzu ana sayarwa tsakanin N300 zuwa N400.
Abin da yafi kamari shine tumatir, barkono da sauran abubuwa masu lalacewa.
A halin da ake ciki, kungiyar Kungiyoyin kwadagon garin Kudu maso Gabas, ASETU, ta bayyana toshewar a matsayin wata kyakkyawar dama ga mutanen yankin na Kudu maso Gabas don bunkasa noma da samar da karin abinci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More