Farashin shikafa zai sauka – Atiku Bagudu

Gwaman Jahar Kebbi Atiku Bagudu ya bayyana cewa yadda manoma suka yi noman shinkafa a daminar bana, zai taimaka wajen daidaita farashin shinkafa a kasuwannin na Najeriya.

Bagudu shi ne shugaban Kwamitin noman shinkafa da Alkama na fadar shugaban kasa a Najeriya, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a karamar hukumar Argungun a jahar  yayin da yake ganawa da manoman shinkafa na yankin.

Gwamnan Bagudu ya tabbatar da cewa yawan shinkafar da aka noma a daminar bana, zai taimaka matuka wajen rage farashin tsadar shinkafa a Najeriya, tare da dakile shigo da shinkafar kasar waje a cikin kasar.

Bagudu ya shaidawa manoman cewa gwamnatin jahar bada jimawa ba za ta siya kayayyakin tasar shinkafar kuma ta rabawa manoman domin ganin an bunkasa gyaran shinkafar dan kaiwa kasuwanni.

Tuni  dai aka horas da matasa yin amfani da kayayyakin da zai taimakawa manoma a dukkanin kananan hukumomin jahar 21.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More