Fasto Biodun ya ajiye mukaminsa na coci kan zargin Fyade

Duk da  cewa wasu magoya bayan Fasto Biodun Fatoyinbo suma sun fito sunyi  zanga- zanga kan zarge da Bisola ta masa nayi  mata ‘fyade’ lokacin tana ‘yar shekara 16, ya ce ya dauki matakin ajiye mukaminsa na cocin Commonwealth of Zion Assembly COZA.

A sanarwa da ya wallafa a yau Litinin 1 ga watan Yuli 2019 a shafinsa na Instagram, Fasto Biodun, ya ce, ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da jagororin addinin kiristanci na duniya.

30 ga watan Yuni  ne  masu fafutuka suka yi zanga-zanga a Abuja da Legas da manufar bayyana wa mutane irin barnar da wasu fasto-fasto ke yi a majami’u.

Masu fafutukar na kara kira ga mata da su fallasa masu irin wannan ta’ada kasancewar zamanin danne hakkin mata ya shude.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More