Fatal Arrogance: Ina da-na-sanin fitowa a fim kan ‘yan Shi’a – Yakubu Mohammed

Shahararren tauraron  fina-finan Hausa a Najeriya, Yakubu Muhammad ya ce ya yi nadamar fitowar da ya yi a wani fim wanda ke ci gaba da janyo cece-ku-ce a wasu sassan kasar, mai suna “Fatal Arrogance.”

Bayanai sun nuna cewa an shirya fim din ne shi ne domin nuna yanayin rayuwa ta wata kungiyar Musulmai a kasar ta Najeriya.

Sai dai wani hoto da aka rika yawo da shi a kafafen sada zumunta na intanet ya sa an rinka furta kalaman batanci ga tauraron, da ma sauran wasu taurarin  ta suka fito a cikin shirin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More