Fatal Arrogance: Yakubu Mohammed ya ce a shirye yake ya biya diyya don ganin an goge duk inda ya fito a fim din

Ya shaida wa BBC Hausa cewa ya yi nadamar fitowa a fim din.

“Na gaya wa furodusan ya cire duk inda na fito a fim din, a shirye nake na biya diyya, wanda shi ne abin da doka ta tanada,” in ji shi.

“Ban taba tsammanin fim din za bayyanashi ta wannan hanyar ba. Na yi aiki ne kamar yadda duk wani jarumi ya saba, na bayyana sau shida a wurare daban-daban. A fim din an harbe ni, daga baya na mutu, ”in ji shi.

“Fim ne da ya nuna arangama tsakanin Sojojin Nijeriya da kungiyar Shi’a a Zariya, kuma an kashe ‘yan kungiyar da yawa. Lokacin da na karanta labarin, ban ga wani abin da ke batanci ga addinin Musulunci a ciki ba, amma kun san labarin film zai iya canzawa a kowanne lokaci, abin da ya faru ke nan.

Harkar ta koka a kafafen sada zumunta cewa ta kadu matuka kuma an nuna shugabanta Shaikh Ibraheem Zakzaky da munanan abubuwa a matsayin ‘yan ta’adda.

Fim din, an dauke shi a garin Enugu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More