Fatima Mamman Daura ce ta dauki bidiyon da ake yama-didi dashi – Aisha Buhari

Baraka ta kunno kai a Fadar Shugaban Najeriya a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matarsa kishiya.
A yan kwanakin nan wani bidiyo ya rika yawo a shafukan sada zumunta wanda a cikinsa aka ga uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tana ta fada da harshen Turanci tana gaurayawa da Hausa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun rinka alakanta wannan bidiyon da cewa Aisha Buhari ce ta dawo daga Ingila tana fada cewa an rufe mata kofa.
BBC ta samu jin ta bakin Aisha Buhari inda ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

Ta kuma yi karin haske cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta dauki bidiyon da ake tafka mahawara a kai.
Sai dai ko da BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta musanta daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More