First Lady za a dinga kira na dashi daga yanzu – Aisha Buhari

Mai dakin Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce daga yanzu kada wanda ya kara kiran ta da lakabin ‘Matar Gidan Shugaban Kasa’, sai dai “Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady”. Aisha ta bayyana haka ne a wurin liyafar cin abinci da aka shirya domin girmama matan tsofaffin gwamnoni a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ta ce ta zabi a kira ta da “Matar Shugaban Kasa” ne don radin kanta duk da cewa ya haddasa rudani. “Ni na zabi a kira ni da lakabin “Matar Gidan Shugaban Kasa a 2015 amma ina fatan za ku yafe ni bisa rudanin da ya haifar. Daga yanzu ina so a kira ni da Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady”. Sai dai kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Shugaba Buhari ya bayyana a 2014 cewa zai rushe ofishin First Lady idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Wannan ba shi ne karon farko ba da uwar gidan shugaban ke amfani da tarukan liyafa don isar da sako ba, ko dai ga ‘yan kasa ko kuma mahukunta.

A watan Maris, jim kadan bayan mijinta ya lashe zabe a karo na biyu ta ja kunnen shugabannin jam’iyyar APC mai mulki kan rabon mukamai a wajen liyafar da aka shirya domin murnar nasarar mai gidan nata a Daura

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More