Fitaccen Limamin Kirista,T.B. Joshua, ya mutu

Cocin Synagogue Church Of All Nations (SCOAN) ta ba da sanarwar mutuwar wanda ya kafa ta, sanannen Limamin Kirista, Temitope Balogun Joshua, wanda aka fi sani da T.BJoshua a ranar 5 ga Juni,2021.
Sanarwar ta ce,”Ubangiji ya dauki rayuwar bawansa Prophet TB Joshua zuwa gida – bisa ikonsa kamar yadda ya kamata. Ya mutu ne yana bautar Ubangiji. Wannan shi ne abin da aka halicce shi domin ya yi, kuma shi ya rayu yana yi, kuma ya mutu yana yi.”
An haifi T.B Joshua a ranar 12 ga Juni,1963, ya rasu yana da shekasu 57.
Joshua, fitaccen Limamin Kirista me da me da farin jini a Nahiyar Afrika da Latin America,sakamakon ayyukansa na wa’azi da taimakon marassa karfi.
Mabiyan Limamin Kiristan da wa’azinsa ke haifar da ce-ce-ku-ce na kafar sada zumunta na Facebook sun kai 3,500,000 ,yayin da mabiyansa a kafar YouTube suka zarce 1,000,000, wacce aka ayyana a matsayin wata kafa ta coci da aka fi kalla a YouTube kafin a dakatar da ita.
Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar yabo ta OFR a 2008.
A shekarar 2011, Forbes, ta bayyana Joshua a matsayin Limamin Coci na uku mafi arziki a Najeriya ,duk da shike cocin sa ta yi hanzarin karyata hakan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More