Ga jerin wasu daga cikin muhimman al’amura da suka faru a cikin watan Ramadan a tarihin Musulunci

1 ga Ramadan, aka haifi Sayyid Abdul-Qadir
Gilani.

2 ga Ramadan,aka saukar da At-Torah (Tawrat) ga annabi Musa (A.S).

10 ga Ramadan, Nana Khadijah bint Khuwaylid – matar annabi Muhammad (S.A.W)- ta yi wafati.

12 ga Ramadan, aka saukar da Injila ga annabi Isa(A.S).

15 ga Ramadan, aka haifi Hasan ibn Ali (R.A), jika ga ma’aiki (S.A.W).

17 ga Ramadan, Aisha bint Abu
Bakr (R.A)– matar annabi Muhammad (S.A.W)- ta yi wafati.

17 ga Ramadan, Ruqayyah (R.A) ,diya ga annabi Muhammad (S.A.W) da Nana Khadija,mata ga Uthman bin Affan (R.A), ta yi wafati.

17 ga Ramadan, aka yi yaƙin Badr .

18 ga Ramadan, aka saukar da Zabura ga annabi Dawood (A.S).

19 ga Ramadan, aka sari Ali bin Abu Talib (R.A) da takobi a ka.

20 ga Ramadan, aka yi Fatahu Makkah.

21 ga Ramadan, Ali bin Abu Talib (R.A) ya yi wafati sakamakon raunukan da ya ji lokacin da aka sare shi da takobi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More