Ganduje da Sanusi: Shin Kauran Bauchi na iya kawo karshin rikicin?

Gwamnan jahar Bauchi, Abdulkadir Bala Muhammed  wato  Kauran Bauchi, ya kuduri aniyar ganin an kawo daidaito a rikicin da ya faru tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.

Kauran Bauchin ya yi wannan furucin ne a fadar gwamnatin jahar Bauchi, a lokacin da tawagar da sarkin Kano ya tura bisa jagorancin Makaman Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, domin Kai ziyarar taya shi murnar nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jahar Bauchi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More