Ganduje ya taya gwamnoni 3 murnar samun shugabanci

Gwamnan Jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya gwamnoni 3 murna samun shugabancin kungiyoyin na Najeriya.

Gwamnan Jahar Ekiti Kayode Fayemi, bisa zabensa da aka yi a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnoni, gwamna Jahar Filato Samuel Lalong , a matsayin Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa sai kuma  gwamnan jahar Kebbi  Atiku Bagudu a matsayin sabon Shugaban kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC.

Ganduje ya bayyana cewa, zabar mutum a irin wadancan mukamai na da alaka da cikar dukkan kyawawan halaye na jagoranci, ya kara da cewa cancantarsu da nagartarsu da gaskiyarsu da kuma mayar da hankali wajen samun nasara iri guda na ciyar da kasar nan gaba ne yasa aka zabe su,inda yakara tabbatara ta cewa gwamnatin APC zata kara himma wajen cigaba da gudanar da kyawawan ayyukkan da ta fara tun a shekarar 2015 a duk matakan jahohi zuwa gwamnatin Tarayya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More