Ganduje ya yi kira ga abokan hamayya su zo su hada hannu dan cigaban Kano

Gwamnan dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga abokan hamayya da su zo su hada hannu domin kawo wa jahar Kano cigaba. Ya bayyana haka ne wata sanarwa jim kadan bayan Kotun Koli a na yau Litinin.

Sakataren watsa labaran na gwamna wato Abba Anwar ne ya fitar sanarwar inda yake kuma mika godiya ga al’ummar jahar Kano da suka dage wajen gudanar da addu’o’i domin ganin samun nasarar jamiyyar ta APC a Kano.

Ya kara da yabawa alkalan kotun wadanda suka gudanar da shari’ar, inda ya bayyana cewa hakan na nuna jajircewar bangaren shari’ar wajen kawo ci gaba ga dimokradiyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More