Gara yin bara da Coronavirus ta kashe mutum- Gwamna Elrufa’i

Gwamnatin jahar Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake rufe jahar saboda tashin alkaluman mutanen da  Coronavirus ta  kama a baya-bayan nan, “saboda mutanen ba sa bin doka”.

Yayin zantawa ta musamman da BBC, Gwamna Nasir Elrufa’i ya bayyana fargabar kada karuwar annobar ta fi karfin asibitocin Kaduna bisa la’akari da ganin yadda kwayar cutar ke kara yaduwa.

“Ranar Juma’a za ka ga mutane sun yi cunkoso, to, idan muka ce za mu bude masallatan khamsus salawat wannan cunkoso za a ci gaba da shi, ba a bin doka, ba a bin tsare-tsare,” in ji gwamna.

Ya ce gwamnati ta umarci mutane su rika sanya takunkumi a duk lokacin da suka fito daga gida, “amma mutane sun ƙi ji”.

Yanzu in ka fita kana garin Kaduna, mun ce duk wanda ya fito daga gidansa, ya sa takunkumi, ya sa facemask, mutane ba sa sawa, cewar Elrufa’i. “In ka tsayar da mutum ka ce ya bai sa ba. Sai ya fito da ita daga aljihu. (Ya ce) yana da ita”.

Gwamnan ya ce takunkumin wata kariya ce daga kamuwa daga ƙwayar cutar korona, kuma yana hana yaɗa cutar ga wasu mutane, idan mutum na ɗauke da ita.

An kuma tambayi Nasir Elrufa’i kan sane da halin da jama’arsa ke ciki musamman ma ‘yan kasuwar jihar da ake ta rade-radin cewa sun fara bara, sai ya ce: “Sun fara bara?” Amma ai gara yin bara da mutuwa, in ji shi.

“Gara kai bara kana da rai, da ka mutu… Hakkin da Allah ya dora mana a jahar nan, (shi ne) mu kare lafiya da rayukan dan’adam.

Masu kasuwanci za a iya tallafa musu,” cewar Malam.

Idan komai ya koma daidai, za mu samu yadda za mu tallafa musu domin a koma harkokin kasuwanci kamar yadda aka saba a baya, gwamnan ya alkawarta hakka.

Gwamnan dai ya shafe kusan wata guda yana jinyar cutar korona bayan ya kamu a ƙarshen watan Maris, kafin sanar da warkewarsa daga bisani.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ke fitarwa a kullum sun bayyana gano masu cutar Coronavirus 54 ranar Juma’ar da ta gabata.

A cikin kwana uku na baya-bayan nan kadai, cCoronavirus  ta kama mutum 95 a jahar Kaduna, kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More