Gareth Bale ya dawo Madrid

Dan wasan gaban na Wales din ya isa babban birnin Spain ne a daren Lahadi, ‘yan sa’o’i kadan bayan ya zira kwallaye a wasan da Spurs ta doke Leicester.
Yan awanni kaɗan bayan ya zura kwallaye biyu a wasan karshe na na gasar Firimiya ta bana da Tottenham ta doke Leicester, Gareth Bale ya koma Madrid a jirgin yan kasuwa, a cewar El Chiringuito de Jugones.
Kasancewar Bale a cikin babban birni ya haifar da jita-jita amma dalilin da yasa ya dawo shine don ya iya ganin iyalinshi da ke zaune a Madrid.
Abin fahimta ne cewa idan kakar wasan gasar cikin gida ta kare, zai so ganin matarsa ​​da ‘ya’yansa kuma ya yi ‘yan kwanaki tare da su kafin ya shiga cikin tawagar Wales don buga gasar Euro a watan gobe.
Abin da zai faru a gaba ga Bale ya kasance mara tabbas. Aron sa da aka bayar ga Tottenham ya zo karshe kuma kamar yadda shi da kansa ya fada bayan wasan Leicester, yanzu ba lokaci ba ne na yin kowacce irin sanarwa.
“Za a yi ta ne (sanarwar)bayan Euro. Na san abin da nake yi amma zai iya haifar da rudani idan na ce komai yanzu, “in ji shi bayan kammala wasannin kakar tare da jefa kwallaye biyu a ragar Leicester kuma ya baras da damar da Foxes din ke da ita na samun damar zuwa Gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.
” yanzu, banyi tunanin komai ba sai Wales kuma in kawo karshen kaka a hanya mafi kyawu, “in ji Bale a hirar da ya yi da kafar Sky Sports.
Bale ya kammala kakar wasa ta bana tare da buga wa Tottenham wasanni 34 ne kawai, ya zura kwallaye 16 a raga tare da taimaka wa a jefa kwallo uku a raga.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More