
Gasar Zakarun Turai
Barcelona ta gaza jefa kwallo a raga duk da hare-hare 25 da ta kai zuwa ragar Lyon, yayin da ita ma Liverpool ta barar da damarmakinta.
Lyon 0-0 Barcelona
Liverpool 0-0 Bayern Munich
Rabon da Barcelona, wadda ke jagorantar teburin gasar Laliga da tazarar maki 7 tsakaninta da ta biyu, ta lashe gasar ta Zakarun Turai tun a 2015 da ta doke Juventus a wasan karshe.
Barcelona zata karbi bakuncin Lyon ranar Laraba 13 ga Maris a filin wasa na Camp Nou.
A wasannin da za a buga yau a gasar Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Juventus yayin da Schelke zata fafata da Manchester City da karfe 9:00pm.