Gaskiya lamarin batun jita-jitan auren Shugaba Buhari da Sadiya

BBC ta samu bayanai daga wani makusancin fadar shugaban kasar wanda ba ya so a bayyana sunansa kuma ya musanta wannan labari.

“Zancen kara auren Shugaba Buhari ba gaskiya ba ne. Ba haka zancen yake ba,” a cewarsa.

Sai dai ya ce matar shugaban kasar Aisha Buhari ta dade ba ta kasar. Asali ma, cewa ya yi ta shafe wata hudu a birnin Landan.

Majiyar ta ce an dade ana ‘takun saka’ tsakanin shugaban da matarsa, kuma watakila abin da yasa taki dawowa gida kenan .

Dangane da bidiyon da ya nuna wata mata tana fada a cikin wani gida kamar Aso Rock, majiyar ta tabbatar da cewa Aisha Buhari ce.

Sai dai majiyar ta ce tsohon bidiyo ne kuma an fi shekara biyu da daukarsa.

Kawo yanzu dai, fadar Shugaban Kasar ba ta ce komai ba kan wanna batun, haka ita ministar ba ta fitar da wata sanarwa don musantawa ko tabbatar da lamarin ba.

Sai dai Minista Sadiya Umar Farouk ta wallafa wasu hotuna da sakonni a shafinta na Twitter a ranar Alhamis da ke nuna cewa tana birnin Geneva don halartar wani taro.

Abin da kuma ke kara nuna cewa zancen auren ba gaskiya ba ne – tun da zai yi wuya a daura aurenta ba ta kasar, sannan kuma bidiyon da ake cewa na bikinta ne sun tabbata ba gaskiya ba.

Wasu daga cikin bidiyon ma an dauke su ne, lokacin da take murnar rantsar da ita a matsayin minista.

Hukunci

Daga bayanan da BBC ta tattaro daga majiyoyi da dama a fadar shugaban kasa, sam babu kanshin gaskiya game da batun cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kara aure a ranar Juma’a 11 ga watan Oktobar 2019.

Sai dai kuma majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa akwai ‘rashin jituwa’ tsakanin matar shugaban, watau Aisha Buhari da wasu daga cikin dangin shugaban a waje daya – da kuma wasu makarrabansa a fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock.

Hakan kuma na da nasa ba da shawarar da Aisha Buharin ta yanke na shafe watanni da dama a kasar waje a maimakon kasancewa tare da maigidanta a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More