Gobara ta cinye Na’urar Zabe Kurmus A Ofishin INEC Na Anambara

Kasa da kwanaki biyar zuwa ranar da za a gudanar da zabukkan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa, wata ta tashi a ofishin hukumar INEC na jahar Anambara a yau Talata 12 ga watan fabrairu  wutar ta kone wasu kwantainoni biyu da suke shake da na’urar zabe kurmus.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, jami’an kashe gobara na jahar Anambara suna ta kokarin ganin sun kashe wutar, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, jami’an tsaron farin kaya na DSS da sauransu sun yi wa wajen da gobarar ta tashi kawanya, saboda gudun afkuwar wani al’amari na daban, musamman da yake a ofishin hukumar zabe ne.

A daidai lokacin da yake tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban hukumar INEC na jahar Anambara  ya ce,  zuwa yanzu hukumar  ba za ta iya tabbatar da asarar da wutar ta jawo ba, saboda har yanzu ba a samu nasarar kashe wutar ba, amma dai tabbas na’urar zabe da takai yawan kwantaina biyu ta kone kurmus.

Ban san mai ya jawo gobarar ba, duba da cewa nan muka saba adana dukkan kayan zabe masu muhimmanci tun daga shekarar 2011, don haka ba sabon abu bane ajiye kaya a cikin kwatainar. Inji shugaban hukumar

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More