Gobe za a tashi da Azumin Ramadan a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya ce sai ranar Lahadi za a yi Sallar Idi a Najeriya sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a kasar.
Saboda haka ranar Asabar za a tashi da Azumi kuma shine na 30 ga watan Azumin Ramadan.

Fadar mai alfarma da kuma kwamitin ganin wata na kasar ta Najeriya  ba su samu labarin ganin watan Shawwal na shekarar 1441 ba daga ko’ina a fadin kasar ba,a yau  Juma’a 22 ga watan Mayu 2020, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Hakan ne ya sa Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Majalisar Koli ta Addinin Musulunci suka yanke cewa ranar Lahadi 24 ga watan Mayu wadda ta yi daidai da 1 ga Shawwal 1441 ce ranar Idi a Najeriya.

Sai dai makwabciyar Najeriya, Jamhuriyar Nijar ta sanar da ganin watan na Shawwal inda za a yi Idi a gobe Asabar.

Hakkan bashi ne  karon farko da ake samun babban ba, a  tsakanin kasashen duniya dangane da ganin wata na fara Azumin Ramadan da kuma kakare shi.
Kasar Saudiyya ma dai  ta bayyana cewa ba ta ga jaririn watan Shawwal ba a saboda haka za a yi Sallah ne ranar Lahadi idan Allah ya nuna mana.

Kasar saudiyya ta fara sanar da hakkan ne kafin kasar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More