Goodluck ya yafewa Aminu dan marigayi Shehu Shagari

Tsohon shugaban kasar Najeriya ya yafewa dan  marigayi tsohon shugaban kasa shehu Shagari, wato Aminu Shagari tare da yin godiya bisa hakurin da ya bashi.

“Ina godiya da hakurin da ka bani, dama can ban taba yin fushi da wani ba. Ni dai abunda na yarda  Alkalami ne ni a hannun Allah. Dan haka bani da wani makiyi da zanyi fada dashi, saboda ina da yakinin cewa, duk wani abu da mutane zasu mini sai da yarda Allah. Ina yin kira a gare ka, da ka cigaba da yin koyi da dabi’u mahaifin ka Marigayi  Shehu Shagari, wanda bashi da bangaranci. Allah ya maka albarka.GEJ.” Kamar yadda tsohon shugaban GoodLuck Ebele Jonathan ya wallafa a shafin sa na Facebook.

Dan marigayi shugaban Najeriya  Shehu Sagari, Aminu Shagari ya fito ya bawa tsohon shugaban kasar GoodLuck Ebele Jonathan hakuri a bayyane a makon daya gabata.

Honarabul Shagari Aminu wanda yai dan majlisar wakilai har sau uku, ya kasance daya daga cikin wayanda suka juya wa Jonathan  baya, inda yace ya taimaka wajen kauda gwamnatin Janathan dan ganin shugaban Muhammadu Buhari ya samu nasara, duk da cewa lokacin da yake matsayin sa na jami’in soja yayi jagoranci wajen tumbuke baban sa a shekarar 1983.

#OakTV #OakTVHausa
#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More