Gwaman Bala Muhammad  na Bauchi ya warke daga cutar Coronavirus

Gwamnan jahar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga coronavirus bayan da sakamakon gwajinsa  na biyu ya fito kuma ya nuna baya dauke da cutar ta Covid 19

Gwamna ne  ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Aprilu 2020.

Ga sakon:
 ”Alhamdulillah. Yanzun nan na samu sako mai dadi. Gwajina na biyu na coronavirus ya nuna na warke.
”Na gode muku dukka da adduo’inku da goyon bayanku. Sannan na gode wa Allah – Mai Rahama Mai Jin Kai.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More