Gwamana El’Rufa’i ya fatataki masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi artabu da masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.

Masu tsaron gwamnan ne suka tarwatsa masu garkuwa da mutanen inda suka arce tare da nufa cikin daji.

Jami’i mai hudda da jama’a na gwamnan, Samuel Aruwan ne ya shaidawa BBC aukuwar lamarin.

Da aka tambaye shi ko hakan zai iya jawo wa jahar ja baya daga hannun masu saka hannun jari sai yace “Wannan shi ne karo na hudu da muke wannan taron, sha’anin tsaro abu ne mai fadin gaske”

Aruwan kuma ya bayyana cewa jami’an tsaron na gwamnan sun yi nasarar “harbar  mutane uku daga cikin masu garkuwa da mutanen.”

Hakan yana faruwa daga lokacin da garkuwa da mutane a kan hanyar ta yi kamari inda a makon da ya gabata aka sace sama da mutum 40 a lokaci daya.

 

 Hakan ne yasa mutanen da dama  suke ci gaba da kauracewa hanyar, suke hawa jirgin kasa domin gudun abun kaje ya dawo na bacin rai.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More