
Gwamna Aminu Tambuwal ya cika alkawari sakamakon hirarsa da dan Jarida
Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya cika alkawarin da ya dauka bayan hirarsa da Sashen Hausa na BBC ta cikin Shirin A Fada A Cika.
Shirin wanda ke bin bahasin alƙawuran da ‘yan siyasa suka yi wa magoya bayansu kafin zabe, ya karbi bakuncin Aminu Tambuwal ranar Litinin da ta gabata, inda aka tambaye shi dalilin da ya sa bai cika alkawarin nada mai ba shi shawara kan nakasassu ba.
Gwamnan ya amsa da cewa zai cika alkawarin. “Nan da kwana nawa?” Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambaye shi. “Nan da kwana biyu,” in ji Tambuwal.
A karshe dai gwamnan ya nada Abdulazeez Ibrahim Abdullahi – wani mai bukata ta musamman – a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin masu buƙata ta musamman, abin da ba a saba gani ba.
Abdulazeez ya shaida wa BBC cewa tuni ‘yan uwansa masu bukata ta musamman suka hada masa walima tare da bayyana masa bukatunsu.
“Na je na tambayi mabarata dalilin da ya sa suke yin bara kuma sun shaida mani cewa in suka samu sana’o’in hannu ba za su sake yin barar ba sannan kashi 20 cikinsu karatu suke so,” in ji shi.
“Yadda aka saba shi ne, sai dai a ɗauko wani wanda lafiyarsa ƙalau a ba shi [wakilcin nakasassu].”