Gwamna El-Rufa’i ya bawa Sanusi mukami a jahar Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir el-Rufai ya bai wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukami a hukumar bunkasa zuba jari ta jahar.
Gwamnan na jahar Kaduna, ya nada Sanusi a matsayin mataimakin shugaba a majalisar magabata ta hukumar bunkasa zuba jari ta jahar wadda ake kira KADIPA.

Bayan kwana daya da gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi daga gadon sarautar Kano.

Sanarwar ta kuma bayana cewa gwamna Nasir el-Rufai na cewa martaba ce ga jahar ta samu mutum mai girma irin Sanusi ya jagoraci ci gabanta.

Malam Muhammadu Sanusi II ya yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya wata CBN, kafin ya zama Sarkin Kano a shekarar 2014.

Zuwa yanzu dai ba’aji ta bakin tsohon sarki Sanusi ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More