Gwamna El’Rufai ya samu nasara a kotun koli tara da wasu gwamnonin Najeriya

Kotun koli ta Najeriya ta tabbatar da zabukan wasu gwamnaonin kasar na zaben da aka gudanar a watan Maris 2019.
A ranar Laraba 18 ga wata ne tawagar alkalai bakwai na kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Mary Odili ta tabbatar da nasarar Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jahar Kaduna da Abdullahi Sule a matsayin zababben gwamnan jahar Nassarawa.

Mai Shari’a Mary Peter-Odili ta ya watsi da daukaka karar da David Ombugadu na jam’iyyar PDP ya yi na kalubalantar zaben Gwamna Sule.

Alkalan sun ce mai daukaka karar da jam’iyyarsa ta PDP ba su da kwararan hujjoji.
Kazalika kotun ta tabbatar da nasarar gwamnan jahar Legas Babajide Sanwo-Olu bayan ta yi watsi da kararrakin da aka shigar masu kalubalantar zabensa.
Kotun ta kuma tabbatar da nasarar Seyi Makinde a zaben gwamnan jahar Oyo.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More