Gwamna ganduje ya amince a yi Sallar Juma’a da Idi a Kano

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aminci da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma’a da kuma Idi.

Mai magana da yawun gwamna kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai,ya fitar da sanarwar cewa, gwamna Ganduje ya bayar da umarnin ne bayan ya tattauna da wakilan Malamai guda 30 da kuma wasu jami’an gwamnatinsa a yau Litinin 18 ga watan Mayu 2020. “An umarci Malaman Masallatan Juma’ah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka takumkumi wato face mask da kuma wanke hannaye da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso”, cewar sanarwar.

Gwamna ya kara da cewa, ba za a bari mutane su yi shagulgulan ba lokacin Sallar Idi, kumagwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da dokar ta hana fita don gudun yaduwar cutar ta Covid19
Gwamnatin jahar Kano dai ta bi sahun wasu jahohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma’a da kuma sallar Idi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More