Gwamna Ganduje ya bukaci hukunci kisa ga masu satar mutane a Kano

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar ya bai wa ma’aikatar shari’a umarni da ta yi wa dokokin jahar kwaskwarima domin zartar da hukuncin kisa ga masu satar jama’a.
 
Gwamna Ganduje ya ce wannan ce kawai wata hanya da za a iya magance yawaitar salwantar mutanen musamman kananan yara da akwanakin kadan da suka wace ake sacewa a fadin jahar ta Kano.
A yanzu dai hukuncin masu satar jama’a a jahar shi ne daurin rai da rai.
 
Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake rantsar da kwamitin da jahar ta kafa domin bincike kan hakikanin abin da ya faru dangane da wasu kananan yara guda 9 da rundunar ‘yan sandan jahar ta ceto daga jahar ta Anambra.
 
A makon da ya gaba ne dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ceto yaran guda 9 wadanda ta ce wasu ‘yan kudancin kasar’ ne suka sace suka kuma sayar da su a jihar Anambra, inda aka sauya musu suna da addini.
Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin bai wa yaran da aka ceto din ilimi har zuwa matakin jami’a a kyauta, tare da naira miliyan 1 ga iyayen yaran 9 da ka sace.
Alkaluma na nuna har yanzu ana neman yara fiye da 40 da suke kyautata zaton an sace su ne.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama a jahar Kano sun lashi takobin bin kadin wannan batu na zargin satar yara daga jahar da yadda ake sauya musu sunaye tare da sayar da su ga ma’auratan da ke bukatar ‘ya’ya.
Iyayen da suka ce an sace masu yaransu, sun kafa wata kungiya ta fautukar ganin an karbo musu yaransu kuma sun shaida wa BBC cewar sun rasa yara sama da arba’in, yayin da suka kara da cewa a kullum suna cikin zulumin halin da ‘ya’yan nasu ke ciki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More