Gwamna Ganduje ya fitar naira miliyan 880 don gyara makarantun Kano

Gwamnatin jahar Kano ta ce a kwanan nan ta fitar da kudi naira miliyan 880 don gyara wasu makarantu a fadin jihar gabanin za’a bude makarantu.

Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Nasiru Gawuna ya wakilta, ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa a ranar Asabar.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Hassan Fagge, ya raba wa manema labarai a Kano ranar Lahadi.

Ya ce a wani bangare na bin ka’idojin cutar COVID-19, an gudanar kayan kariya na sirri da aka samar wa makarantu a fadin jihar.

Ganduje ya bayyana manufofin gwamnatin tarayya a kan ilimi a matsayin kayan aiki na hakika don ci gaban kasa.

“Ina son in amince da kokarin da gwamnatin tarayya ta yi a bangaren ilimi, musamman a wannan lokacin da za a bude makarantu,” kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa.

Tun da farko a cikin jawabin nasa, Nwajiuba ya ce ya je Kano ne don taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso yamma don yin nazari kan ka’idoji da ladabi na sake bude makarantu.

Ya ce yayin ziyarar, zai kuma tantance abubuwan da ke cikin makarantun da nufin tabbatar da cewa suna aiki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More