Gwamna Ganduje ya gabata da kasafin kudin 2020

Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudin Shekara ta 2020 na Naira Biliyan 197,683,353,659 wanda aka yi wa lakabi da “Dorewar Harkokin Cigaban Jahar Kano wanda ya gabatar gaban Majalisar dokokin Jahar Kano a ranar Alhamis din nan.

Kasafin kudin ya zarta na shekarar da ta gabata da sama da Naira biliyan 40, ya kunshi Naira biliyan 177.7 wanda aka ware wa ayyuka na Musamman, ya yinda ayyukan yau da kullum aka tsara za su lakume Naira Biliyan 79.10.

Gwamna Ganduje ya jinjina wa mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna bisa kyakkyawar biyayyarsa, inda ya ce kyakkyawan hadin kai shi ne abin da ake fatan fara samu, kuma an hakikance cewa idan aka samu cikakken hadin kai ne kawai Gwamnati za ta samu cin nasarar habaka harkokin cigaban al’umma.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More