Gwamna Ganduje ya nada Sarki Sanusi  shugaban majalisar sarakunan Kano

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Ganduje, ya nada Sarki Muhammadu Sanusi II, shugaban majalisar Sarakunan jahar Kano. Gwamna  Ganduje ya nada Sarkin Birni, Malam Muhammadu Sanusi II a kan kujerar Shugaban Sarakunan jahar, bayan gwamnatin Ganduje ta kafa sababbin Masarautu.

Sanarwar ta  fito ne daga  bakin babban sakataren yada labarai na  gwamnan jahar Kano  wato  Abba Anwar, inda  ya bayyana cewar  nadin ya dogara ne da sashe na 4(2) (g) da sashe na 5(1) (2) na dokokin masarauta.

Dokar masarauta da aka rattabawa hannu kwanaki 5 da suka wuce ta bawa gwamna Ganduje, damar nada sarkin da zai jagoranci zaman sauran sarakunan da ke karkashin majalisar sarakuna ta jahar Kano.

Matsayin na sarkin birni, wanda aka nada Sarki Sanusi ya fara aiki ne daga yau Litinan 9 ga watan Disamban 2019.

Abba Anwar ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya umarci sarki Sanusi  da  yayi gaggawar kiran taron farko na sarakunan jahar kamar yadda dokar ta tanada.

Karmar dai yadda aka sani sabbin sarakunan na Kano su ne Alhaji Aminu Ado Bayero sarkin  Bichi, Dr. Tafida Abubakar sarkin  Rano, Alhaji Ibrahim Abdulkadir sarkin Gaya, sai kuma Ibrahim Abubakar II Sarkin Karaye. Wayanda dukkannun su keda daraja ta farko.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More