Gwamna Ganduje ya sayi jirgin ruwa masu mugun gudu wa ma’aikatan lafiya

Gwamantin Jahar Kano ta saya wa hukumar lafiya a matakin farko ta PHCMB kwale-kwale masu mugun gudu domin yin amfani da su wurin kaiwa ga kauyukan da ke tsallaken ruwa.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar Ahmad ya fitar yau Talata 1 ga watan satamba 2020, babban sakataren hukumar na Kano, Dr. Tijjani Hussain ya ce ya zama wajibi ne ga gwamanti ta sayi jiragen don yin amfani da su musamman wurin yin rigakafi a kauyuka.

“Gwamnati ta ga dacewar sayen jiragen ne sakamakon yadda damuna ke haddasa cikar koramu a jahar ta yadda ma’aikatan lafiya za su daina shan wahala wurin isa kauyuka,” in ji sakataren, wanda Dr. Sharif Yahaya ya wakilta yayin karbar jiragen.

Ya ce mazauna kananan hukumomin Dawakin Kudu da Bagwai ne za su fara amfana da “cigaban” kafin a kai ga sauran yankunan jahar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More