Gwamna Ganduje ya shirya tsaf dan kafa majalisar Sarakuna a Kano

Gwamna jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje Kano ya umarci kwamishinan ayyuka Mu’azu Magaji, ya gyara ofishin majalisar sarakuna, Gidan Shettima, wanda yake a farfajiyar fadar Sarkin Kano.

Babban sakataren yada labarai na Gwamna Abba Anwar, ya fitar da sanarwar cewa, umarnin alamu ne dake nuna cewa rantsar da sarakunan za a yi shi nan ba da dadewa ba.

Gwamna ya bawa kwamishinan umarnin tabbatar da an gaggauta gudanar da aikin gyaran gidan.

Tuni dai aka duba gidan Shettima don gano yanayin gyaran da za a yi. “Ba gyara kadai ba, inason ganin aiki mai inganci. Saboda jahar Kano ta cancanci hadaddiyar majalisar sarakuna,” ya kara da cewa.

Hakkan dai yana nuna cewa tuni dai gwamna Ganduje ya shirya tsaf wajen kafa majalisar sarakunan a jahar Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More