Gwamna jahar Borno ya bawa kabilal Igbo da Yarabawa mukami

Gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zulum ya rantsar da wasu mutane biyu da suka hada da kabilar Igbo da wani Bayerabe a matsayin masu ba shi shawara ta musamman a gwamnatin tasa.

Kakakin gwamnan Isa Gusau, ya bayyana  cewa ranar  Laraba 29 ga watan Janairu ne gwamnan ya rantsar da Chief Kesta Ogualili daga jahar Anambra da kuma Alhaji Yusuf Alao daga jahar Oyo, tare da mutane ashirin da hudu.

Tsawon shekaru suka  dauka wajen taka muhimmiyar rawa a siyasar jam’iyyar APC ta jahar Borno, cewar sanarwar.

Mataimakin gwamnan jahar Umar Kadafur ne ya wakilci gwamna Zulum a wajen taron rantsar da su, inda ya bukaci da su za zage dantse wajen ganin sun tabbatar da samar da cigaba a jahar ta Borno.

 Yayin da dukkaninsu suka yi  alkawarin yin aiki tukuru domin  tabbatar da nasarar ga jam’iyyar APC da kuma gwamnatin jahar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More