Gwamna Obaseki na da damar komawa APC idan har yana so – Gwamna Wike

Menene ra’ayinku game da hakan?

Gwamnan jahar Rivers Nyesom wike ya bayyana cewa, gwamna Godwin Obaseki, wanda ya samu nasarar  lashe zaben gwamnan jahar Edo  da aka gudanar a ranar  Asabar,  karkashin inuwar jam’iyyar People Democratic  Party (PDP) yana da damar da zai koma jam’iyyar All Progressive  Congress (APC), idan har yana ganin PDP ba ta masa abunda ya kamata ba

Gwamna Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin din  Channel a safiyar yau Juma’a 25 ga watan Satamba 2020.

“Bana son nayi  wata maganar da zata kasance  ba mai yuwuwa ba, a dauka cewa hakan ta kasance, to sai me?  Siyasa kanan”inji gwamna Wike  bayan da aka tambaye shi ya zaiyi idan Obaseki ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC duba da cewar ya samu nasara ne a karkashin jam’iyyar tasu.

Gwamna Wike ya kara da cewar, idan gwamnan ya yarda cewa  yanzu PDP ba jam’iyyar da zai tabbatar da manufar sa bace, babu wani damuwa. Amma ban yarda hakan zai faru ba domin gwamnan yace mana babu yadda za a yi ya bar jam’iyyar ta PDP. Idan ya bar jam’iyyar, mutanen Edo baza su ji dadin yin hakan ba.

A karshe  Wike ya ce ya PDP ce  jam’iyyar da tayi wa Obaseki sutura kuma ta sanya masa lema yayin da ake ruwa, don haka ya  tabbata bazai bar jam’iyyar  ba.

Gwamna Wike shine shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jahar ta Edo

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More