
Gwamna Ortom ya bukaci a baiwa masu hankali lasisin mallakar AK47 don kare kansu
Gwamnan jahar Binuwai,Samuel Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya ta bai wa `yan kasar da suka mallaki hankali lasisin mallakar bindiga kirar AK47 domin su kare kansu daga hare-haren da miyagu ke kaiwa a sassan kasar ta Najeriya.
Gwamnan ya ce ba da lasisin ne kawai mafita, saboda manyan makaman da ke hannun miyagu sun fi karfin bindigar da doka ta ba da izinin mallaka.
Gwamnan Ortom ya yi bayyana hakkan ne yayi wani jawabi da ya gabatar a wani taron gwamnonin Najeriya da aka gudanar ta intanet.
Inda ya kara da cewa jami`an tsaron Najeriya na bakin kokarinsu, amma aiki na nema ya gagari kundila idan aka yi la`akari da hare-haren da `yan boko haram, `yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kaiwa sassa daban-daban a kasar ta Najeriya.
Idan gwamnati ta ba da damar lasisin, mutane za su samu damar ajiye bindigogin a gidajen su, kamar yadda miyagun ke dasu, ta yadda za su iya tunkarar miyagun idan har suka kai musu hari”, in ji Gwamna Ortom.
Sai dai Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce ba alheri ba ne batun.