Gwamna Wike ya fashe da kuka bayan ya samu nasarar lashe zabe

Laraba 3 ga watan Afrilu hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta Jahar Ribas ta bayyana dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP, Nyesom Wike a matsayin wanda ya lashe zaben na jahar Ribas.

Baturen zaben,Teddy Adias, shi ne ya bayyana sakamokon zaben a shedikwar ofishin INEC dake garin Fatakwal.

Ya ce ya samu  nasarar lashe zaben ne da kuri’u 886,264 a yayin da dan takarar gwamna a jam’iyyar AAC, Biokpomabo Awara, ya samu kuri’u 173,859.

Awara ya samu goyon bayan Ministan Sufuri ne wato  Rotimi Amaechi sakamakon rashin dan takara da jam’iyyar APC ta  zamanto  ba ta da shi a Jahar .

A yayin da Shugaban jam’iyyar PDP Secondus, tare  Atiku Abubakar suke kan murna tare da taya Wike murnar nasarar lashe zaben,bayan INEC ta bayyana Wike a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar a Ribas.

Wike ya bayyana cewar zai hada kai  da sauran jam’iyyun adawa  na jahar dan ganin an samu nasarar kawo cigaba a jahar ta Ribas. Inda ya kuma bayyana rashin jin dadin sa kan wayanda suka rasa rayukan, da kuma wayan da suka samu raunuka a yayin da ake gabatar da zaben sabanin banbancin ra’ayi.

A karshe Gwamna wike ya fashe da kuka tare da cewa shifa baya cikin farinciki, sakamakon abubuwan da suka faru a jahar tasa.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More